Dan Na Zagi Shugaban Amurka Sai A Koreni Daga Aiki?

A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne, ‘yan jarida suka dauki hoton wata mata a lokacin da take tuka keken ta a tsakiyar birnin Washington, dai-dai da lokacin da motocin shugaban kasar Amurka Donal J. Trump suke wucewa.

Juli Briskman, ta daga dan yatsan hannun ta na tsakiya ga shugaban kasa, wanda hakan yake nuna alamar zagi, kamfanin da matar takema aiki sun sallameta daga aiki, wanda take ganin cewar wannan ya take hakkinta na ma’aikaciya.

Hakan yasa ta shigar da karar kamfanin, da cewar sun koreta daga aiki ba bisa ka’ida ba, tana ganin cewar babu ruwan aiki da ra’ain mutun, musamman ga rayuwa da ta shafi mutun.

Mr. Steve Herman, daya daga cikin ‘yan jaridun shugaban kasa ne ya wallafar da wannan hoton a kafafen sadarwar yanar gizo jim kadan da faruwar abun, wanda hakan ya ja hankalin jama’a a kasar, a inda wasu ke ganin hakan dai dai ne, wasu kuma na ganin bai kamata a dinga zagin shugabanin ba.