Jaridar Newsweek ta ruwaito cewa, leke-leken wayar abokan zama ka iya jefa mutum zaman kurkuku na tsawon shekara guda ko biyan tarar kudaden Riyal dubu dari biyar kwatancin Naira Miliyan arba’in da bakwai a Saudiyya.
“Ma’aurata da ke shirin binciken wayar juna a Saudiyya su sake tunani, saboda yin haka ka iya kai ga biyan tarar kudaden Riyal dubu dari biyar tare da zaman kurkuku na tsawon shekara guda,” inji sanarwar da Gwamnatin Saudiyya ta fitar ranar Litinin
An dauki wannan matakin ne da nufin kare hakkin masu amfani da yanar gizo da kuma kare tarbiyyar al’umma, a cewar Ma’aikatar Yada Labarai ta kasar.
Facebook Forum