Kamfanin kera motoci na kasar Jamus, Volkswagen ya kashe kudade sama da dala biliyan 7.4 domin fansar motoci masu amfani da man dizel dubu dari uku da hamsin a Amurka bayan da kamfanin ya amsa laifin karya dokar gurbata yanayi. An gane cewa tun a shekarar 2009 kampanin ke sayar da irin wadannan motocin masu fitar da hayakin da ke gurbata yanayi. Wannan ya tilastawa shugaban kampanin yin murabus.
Kotu ta tilastawa Volkswagen fansar ko kuma gyara kashi tamanin da biyar na motocin masu illa kafin wa’adin watan Yunin 2019.
Bayanan kotu na nuni da cewa, zuwa karshen shekarar da ta gabata, kampanin ya fanshi motoci masu amfani da man dizel guda 335,000 inda ta sake sayar da dubu goma sha uku da kuma lalata guda dubu ashirin da takwas. Sannan an ajiye motoci dubu dari biyu da casa’in da hudu a fadin kasar.
Akasarin motocin da aka fansa na nan an paka su a katafaren wajen tattara matattun jiragen sama da ke hamadar jihar California. Kuma babu ranar kwashesu.
Facebook Forum