Jim kadan bayan bayyanar wani katon katako a saman teku, yankin jihar Florida ta Amurka, katakon da aka garzaya da shi gidan tarihi, wanda ya bayyana alamar bangaren jirgin ruwa ne. Ana cigaba da nazarin katakon a dakin ajiyar kayan tarihi.
Masana na nazartar katakon wanda girman shi ya kai kimanin murbba’in kafa arba’in da takwas 48. A cewar jaridar Florida Times-Union, masana a gidan tarihin St. Augustine Lighthouse dake yankin arewacin jihar, suna zurfafa bincike akan katakon.
Wanda alamu suka nuna cewar, wannan katakon na wani jirgin ruwa ne da ya bace tun kimanin shekaru dubu daya da dari bakwai 1,700 da suka wuce, katakon na dauke da nau'in rubutun Roman.
A ta bakin mai magana a madadin gidan tarihin Brendan Burke, alamu sun bayyana cewar jirgin ya hadu da hadarin igiyar ruwa, wanda ta lullube shi ba’a ganshi ba tun a wancan lokacin, amma suna kokarin gano yadda lamarin ya abku, za kuma a sanar ma manema labarai da zarar an kammala binciken.
Facebook Forum