Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karon Farko Tun Shekarar 1938 Ba Alkalin Wasa Daga Burtaniya A Rasha 2018


Hukumar kula da wasan kwallon Kafa ta Duniya (Fifa) ta zabi alkalan wasa 36 domin gasar cin kofin duniya 2018 da za'ayi a kasar Rasha, amma babu mutum daya da yafito daga Ingila, Scotland, Wales ko Northern Ireland.

Wannan shine karo na farko tun shekara 1938 kimanin shekaru 80 da suka wuce, Mark Clattenburg ne kawai yeke jerin sunayen jami'an da Fifa ta lissafa a tsawon lokaci, 2016, daga cikin wanda za zaɓa zuwa don hura wasan a Rasha.

Koda shikea yanzu ya bar aikinsa tare da Firimiya lig sakamakon hakan ya rasa wurinsa inda Hukumar kwallon kafa ta Ingila FA ta kasar Ingila ta nemi hukumar kwallon kafa ta Duniya (Fifa) da ta maye gurbinsa da wani jami'in amma Fifa ta ki amincewa da wannan rokon.

Sai dai tun daga shekarar 1938, ba a yi gasar cin kofin duniya ba har na tsawon shekaru 12 bayan 1938 saboda yakin duniya na biyu, kuma tun lokacin da aka sake komawa a 1950, akan samu jami'i guda daya daga Ingila a kowace gasar. da yake cikin jerin sunayen alkalan wasa amman a wannan karon babu.

Har ila yau, babu wasu jami'an Birtaniya da aka zaba a mataimakan alkalan wasa cikin 63, da hukumar ta Fifa ta bayyana sunansu amman za'ayi amfani da bidiyo mai taimakawa (VAR) a gasar.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG