Damagaran: Malaman Jami'a Na Yajin Aiki

Tambarin Jamhuriyar Nijar

Malaman Jami’ar Damagaram sun fara wani yajin aikin da sai baba ta gani, biyo bayan ire-iren matsalolin da suke fuskanta wadanda suka hada da karancin dakunan karatu da rashin isassun malamai, har ma da makalewar alawus din malaman, dai dai sauransu.

Maga takardar kungiyar malaman jami’ar ta Damagaran Illu Mammna, ya karawa wakilyar Muryar Amurka Tamar Abari haske kan wannan matsaloli. Baya ga wadannan matsalolin gwanati ta rage kudaden da ake baiwa jami’a domin ta gudanar da aikin ta, hakan ne yasa kungiyar suka duba suka ce ba zasu fara aikin sabuwar shekara ba da dinbim bashin da suke bin gwamnati, suna bukatar ayi biyan bashin daddawar kauye wato abiya na baya san nan a karbi wani.

Yajin aiki dai ba fashi inji Dakta Illu Mamman maga takardar kungiyar malaman Jami’ar Damagaran. Ya ci gaba yiwa wakilyar Muryar Amurka bayanin yadda sai bayan da suka kai takardar yajin aikin suka kuma tsunduma cikin yajin aikin san nan aka nemesu aka shaida musu cewa babu wani abu da ya kamata a basu, ganin haka ne yasa malaman ke ganin lalle ba zasu koma kan aikinsu ba.

Suma a nasu bangaren ‘dalibai na ganin wannan yajin aiki ba zai kawo musu komai ba sai ci baya ga neman iliminsu, babbar matsala anan dai itace rashin sanin lokacin komawa karatu. ‘Daliban dai na kira ga gwamnati da ta ‘daki duk matakan da ya kamata domin ganin sun koma karatu.

Saurari rahotan Tamar Abari.

Your browser doesn’t support HTML5

Damagaran: Malaman Jami'a Na Yajin Aiki - 2'29"