Shugaban kungiyar IPOB da ke fafutukar ballewa daga Najeriya Nnamdi Kanu, ya nemi kotu ta mayar da shi gidan yarin Kuje da ke Abuja, babban birnin kasar.
A karshen watan Yuni hukumomin tsaron Najeriya suka kamo Kanu daga kasar waje aka sake gurfanar da shi a gaban kuliya.
Lauyansa Ifeanyi Ejiofor ya shigar da wata bukata a ranar Laraba a gaban kotu inda ya nemi a mayar da shi gidan yari da ke Kuje daga ofishin hukumar DSS, saboda a cewarsa, ana gana masa azaba a kaikaice, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Lauyan ya kara da cewa likitocin da ke kula da lafiyarsa a ofishin na DSS ba su wadatar ba.
Karin bayani akan: Nnamdi Kanu, Ifeanyi Ejiofor, Igbo, Biafra, Biyafara, DSS, IPOB, Abuja, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
A shekarar 2015 aka fara tuhumar Kanu da laifin cin amanar kasa da wasu laifuka masu yawa, amma an ba da belinsa a shekarar 2017.
Nnamdi Kanu dai ya yi ikirarin cewa ana yi wa rayuwarsa barazana ne a lokacin da sojoji suka kai wani samame gidansa, lamarin da ya sa ya tsere daga kasar.
Sai dai lauyansa Ejiofor ya kara da cewa, tun da aka shigo da Kanu cikin Najeriya “ta barauniyar hanya” aka ajiye shi a wani kebabban wuri na kadaici.
Ejiofor ya kuma ce, idan ba a yi hattara an kai masa dauki ba, ran Kanun zai iya salwanta kafin a je yi masa shari’a.
Jaridar Vanguard ta ambato lauyan yana neman kotun har ila yau ta ba likitocin Kanun dama domin su gudanar da cikakken bincike kan lafiyarsa.
Bayan da aka dawo da shi Najeriya, Mai Shari’a Binta Nyako ta ba da umarnin a tsare Kanu a ofishin hukumar tsaro ta DSS har sai zuwa ranar 26 ga watan Yuli da za a ci gaba da shari’ar.
Nnamdi Kanu: An Cafke Shugaban Masu Fafutika Raba Najeriyar, Za a Tuhume Shi
Your browser doesn’t support HTML5