NIGER, NIGERIA - Kungiyar ASUU dai ta share watanni shida ta na yajin aiki a sakamakon takaddamar da ke tsakaninsu da gwamnatin Nigeria.
Farfesa Aliyu Paikon dai ya ce bai gamsu ne da dalilan kungiyar ta ASUU ba na yin yajin aiki. Sannan kuma kalaman da shugaban kungiyar ta ASUU na Nigeria ya yi akan malaman da ke koyarwa a Jami’o’i mallakar gwamnatin jihohi.
To kokarin jin ta bakin shugabannin kungiyar malaman reshen Jami’ar ta IBB ya ci tura. Amma daya daga cikin malaman jami’ar ta IBB Dr. Aminu Aliyu Wushishi ya ce matakin da Farfesan ya dauka na ficewa daga kungiyar ta su baya tare da shi.
Bayanai dake fitowa daga hukumar jami’ar ta IBB na cewa an bada umurnin bude makarantar a ranar 5 watan Satumban nan, to amma kuma wata sanarwar daga kungiyar ta ASUU reshen jami’ar ta IBB ta ce suna tare da kungiyar malaman ta Najeriya.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:
Your browser doesn’t support HTML5