Bayan Kammala zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu a Najeriya, a karshen makon da ke karatowa ne ake sa ran za a gudanar da zaben gwamnoni.
Yanzu haka hankula sun fara karkata kan yadda batun canja sheka ke zama ruwan dare a Najeriya musamman ma tun baya da jam’iyar adawa ta APC ta lashe zaben shugaban kasa.
“Za mu iya kallon haka ta fuska biyu kodai jam’a da dama sun dawo daga rakiyar jam’iyya mai mulki suna shiga jam’iyar APC domin suna so su ba da gudunmuwarsu.” In ji Tukur Abdulkadir, malami a sashen kuyar da kimiyyar siyasa a jami’ar jihar Kaduna.
Haka kuma ya kara da cewa hakan mai yuwuwa na nufin ba a shirye su ke su zauna a bangaren adawa kamar yadda sauran jam’iyun adawa su ka yi na tsawo shekaru 16 ba.
Ya kuma kore fargabar da ake yi na cewa watakila Najeriya za ta koma mulkin jam’iya guda ya na mai cewa yadda PDP ta karbu ta mallake kusan biyu cikin kashin ukun ‘yan majalisu bai hana samar da jam’iyun adawa ba.
‘Yan siyasa da dama a Najeriya na ta ci gaba da komawa jam’iayr APC yayin da ake shirin tunkarar zaben gwamnoni a ranar 11 ga watannan na Aprilu.
Your browser doesn’t support HTML5