Cutar ‘Melanoma’ na daya daga cikin cututtukan daji da ba’a cika mai da hankali wajen basu kulawa da ta kamata ba, “Subungual melanoma” a turance cutar kansa ce da take bayyana a jikin kunbar dan’adam, wanda takan fito kamar wani zane.
Mutane da yawa basa la’akari da ita don daukar matakan da suka kamata wajen magance cutar a matakin farko, wanda rashin yin hakan yakan iya kaiwa ga babbar cutar ta kansa.
A duk lokacin da wani layi mai kalar ruwan goro, ko nau’in ja ya fito a jikin kunbar mutun, hakan yana nuna alamun cutar kansar jiki, kuma yakan iya zama mutun na dauke da cutar a cikin jikin sa, haka a duk lokacin da mutum ya ga wata sabuwar alama ta wani abu da ya fito a jikin kunba, to ya nemi ganin likita don tabbatar da cewar baya dauke da cutar melanoma.
Yana da matukar muhimanci a duk lokacin da mutum ya ga wasu canje-canje a jikin kunbunan sa ya garzaya wajen ganin likitan fata "Dermatologist", don tantance dalilan canje-canjen, da tabbatar da duba lafiyar sa don tabbatar da basu dauke da cutar kansar melanoma.
Binciken ya kara da cewar, a duk lokacin da kuma mutun yaga wasu layuka da suke a kwance, shima hakan yana iya zama mutun ya kamu da cutar ‘Muehrcke’ a turance, wanda yawancin karanci wasu sinadaran gina jikin dan’adam ke haifar da cutar, itama na iya zama cikin jini da cutar da lafiya bil’adama.