Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Google Zai Fara Tantance Mutane Masu Biyan Tallace-Tallacen Siyasa


Kamfanin Google ya bayyanar da cewar zai kara kaimi wajen ganin ya tantance duk wata talla da mutane ke biya ana saka musu a shafin shi, musamman tallace tallace masu alaka da siyasa, kamfanin ya bayyanar da hakan ne a wata sanarwa da aka wallafa a shafin shi na yanar gizo.

Duk wani mutun da yake da bukatar yin wata talla da ta shafi siyasa, za’a bukace shi da ya bayyanar da kanshi, inda za’a bukaci yabada wani kati da gwamnati ta bashi mai dauke da hoto, don sanin wanene shi, kana da wasu bayanai.

Haka kuma kamfanin zai bukaci duk masu siyan talla da su bayyanar da wanda zai biya kudin tallar kamin a bashi damar saka talla, a cewar daya daga cikin shugabanin kamfanin Mr. Kent Walker, mun fito da wannan tsarin ne don tantance wadanda suke biyan tallar siyasa, wanda za’a kirkiri wani runbu da ko bayan shekara nawa ne, mutun zai iya duba talla da kuma bayanan wanda ya biya kudin ta.

Sanarwar tafito dai-dai da lokacin da ake kokarin kafa wata doka don sanin suwa suke biya da daukar nauyin duk wata tallar siyasa, kamar yadda ake dasu a kafofin talabijin, kamfanonin facebook da na twitter suna goyon bayan wannan sabon kudirin.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG