Zulfa’u Musa, wata matashiya mai sana’ar sarrafa gari- dangogin Masara, Dawa, Alkama da kuma garin Kunu duba da yadda mafi akasarin mata masu kananan sana’oi basa wuce sana'a kamar ta tufafi alhalin ta lura da cewar akwai albarka a sana’ar abinci.
Ta ce ta fara sana’ar ne da jarin kudi Naira dubu biyar inda a yanzu jarin nata ya zarce Naira dubu dari, ta dalilin haka ne ta ja hankali mata da su daina raina sana’a ko jarin da zasu soma da shi.
Ta kara da cewa wannan sana’a ta gari da take yi tana zuba su ne a mazubin ledoji inda ta ke kulle su da wani zare wani lokacin takan sa sticker, wani lokacin kuma bata sakawa sakamakon tsoron abinda ka je ya zo daga hukumar NAFDAC.
Zulfau ta ce tana amfani da shafukan sadarwa na whatsapp da sauransu ta hanyar tallata hajar ta ga mutane.
Zulfa’u ta ce duk da cewar ta kammala karatunta na jami’a, hakan bai sa ta hakura da sana’a ba a cewarta a maimakon ta bata dogon lokaci na neman aiki, a hannu guda kuma tana gudanar da sana’arta yadda ta kama, ta kuma bayyana cewa babban burinta a yanzu dai bai wuce ta tabbatar ta samu rajista da hukumar NAFDAC ba.
Daga karshe ta ja hankalin mata da su fara da jari kadan tare da sanya himma da jajircewa domin cimma muradansu.
Facebook Forum