Fiddausi Ibrahim Musa, matashiya da ta ce jajircewa da maida hankali bisa burin da ta sa a gaba ya bata damar cimma burin ta da ta sa a gaba musssaman ma ganin cewar ita mace ce mai naci.
Ta ce da farko ta so ta karanci harkar lauya amma hakkar ta bata cimma ruwa ba sai ta samu gurbin karatu a fannin harkar siyasa a wata jami’a a Illorin, inda ta kammala karatu a wannan fannin.
Bayan kammala karatun jami’a ta sami damar yin aiki a wasu kungiyoyi masu zaman kansu inda ta yi aikin wucin gadi na watanni kafin daga bisani ta samu gurbin karatu a FCDA wato hukumar da ke kula da cigaban babban birnin tarayya Abuja.
Fiddausi, ta ce duk da wannan aikin da take yi ta na aikin wucin gadi a wata kungiya da ke kula da lafiyar bil’adama don kare su daga cutukan da ke kawo matsala ga lafiya ta hanyar amfani da tsirrai da ma abincin mu na gargajiya da suke kara lafiya.
Ta kara da cewa babban abinda ya sa ta samu nasara a harkokin ta na aiki dai bai wuce jajircewarta da mayar da hankali wajen tabbatar da ta cimma nasarar ta a dukkanin abinda ta sa agaba.
Facebook Forum