Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kimiyya Da Fasaha Kan Iya Zama Hadari Ko Alheri Ga Rayuwar Yau Da Kullum


Ana iya kiran wannan ci gaba irin na mai hakar rijiya kuwa? Ganin yadda karuwar fasahar zamani ke kara zama wani abu, da duniya take kara dunkulewa waje guda, domin a yanzu har kasashe masu tasowa a duniya suna samun ci gaban zamani.

Lura da yadda ake samun bunkasa a fannin kimiyya da fasaha a wannan zamani, wasu na dasa alamar tambaya - shin ana iya kiran wannan ci gaban a matsayin abu mai alfanu ga duniya kuwa, lura da yadda yake barazana ga fannonin rayuwar dan adam ta yau da kullum?

Masana na ganin hakan yana iya zama tattare da wasu abubuwa da sai an nutsu kafin a samu amsoshinsu.

Idan muka yi dubi kan fannin bunkasar fannin sadarwa, ana iya amfani da damar wajen aikata barna a doron kasa, ba kawai sai ta satar bayanai ba, ana iya amfani da kafofin wajen ganin an shiga cikin kundin bayanai na kasa wajen sanin sirrinta da duk wasu tsare-tsare da suke da su a bangaren tsaro ga kasarsu.

A cewar shugaban wata cibbiyar bincike Tom Siebel, ci gaban kimiyya da aka samu a duniya na tattare da abubuwan ci gaba kana da na koma baya, domin kuwa, sun nazarci wasu na’urori da suke hade da na’urar zamani, don ganin irin ci gaba da koma baya da ci gaban zai iya haifarwa.

Ya bayyana cewar akwai bukatar tsayawa a binciki yadda ake saka bayanai da sarrafa su a kafar yanar gizo, domin kuwa ta haka ne kawai za’a iya magance wasu matsaloli da ka iya tasowa a kowane hali, idan kuma ba haka ba, ana iya samun matsalar da magance ta zai yi wuya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG