Cutar Ebola ta Kashe Mutane Dubu Hudu da Dari Biyar

Ron Klain, Ebola Czar

Kungiyar Lafiya ta duniya tace ya zuwa yanzu cutar Ebola ta kashe mutane dubu hudu da dari biyar da hamsin da biyar.

Kungiyar Lafiya ta duniya tace ya zuwa yanzu cutar Ebola ta kashe mutane dubu hudu da dari biyar da hamsin da biyar, kuma an tabbatar cewa kusan mutane dubu tara da maitan ne suka kamu da cutar.

Sabon kiyasin da aka gabatar yau Juma'a ya nuna cewa in baicin mutum tara dukkan mutane da cutar ta kashe, ta kashe su ne akasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo.

Tunda farko kungiyar Lafiya ta duniya ta ayyana kasar Senegal a zaman kasar da bata fama da bular anobar cutar, kwanaki arba'in da biyu bayan da jami'an kasar suka bada rahoto mutum guda daya kamu da cutar wanda yayi bulaguro zuwa kasar Guinea.

Yau Juma'a ne kuma shugaba Barack Obama na Amirka ya nada Ron Klain a zaman jami'in da zai lura da yunkurin da Amirka take yi na yaki da wannan cuta.