Babban filin jirgin saman birnin New York ya zama na farko a kasar Amurka da ya fara zafafa matakan gwajin cutar Ebola.
Daga yau Asabar babban filin jirgin saman JFK na New York ya fara gwajin matafiyan dake zuwa Amurka daga kasashen yammacin Afirka na Guinea da Laberiya da kuma Saliyo masu fama da bala'in cutar Ebola.
Jami'ai za su gwada zafin jikin matafiyan dake shigowa, kuma su yi mu su tambayoyin neman gano wasu alamomi.
A mako mai zuwa za a fara irin wannan gwaji a filayen jiragen saman Newark na jahar New Jersey, da Washington, DC, da Chicago a jahar Illinois da kuma Atlanta a jahar Georgia. Daga cikin fasinjojin dake shigowa nan Amurka daga kasashen Afirka masu fama da cutar Ebola, fiye da kashi Casa'in cikin dari na biyowa ne ta wadannan filayen jiragen sama biyar.
A jiya Jumma'a Hukumar Lafiya ta Duniya World Health Organization ko Organization Mondiale de la Santé ta ce wadanda cutar ta hallakasun wuce dubu hudu.
Hukumar ta ce an samu mutane dubu takwas da da dari hudu dake dauke da cutar a kasashe bakwai, kuma mutane dubu hudu da talatin da uku sun mutu sanadiyar ta.