Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Kiwon Lafiya na Kasar Liberiya Sun Shiga Yajin Aiki


Masu aikin ebola a Liberiya
Masu aikin ebola a Liberiya

Yayin da kasar Liberiya ke fama da cutar ebola wadda ta hallaka dubban rayuka a kasar, ma'akatan kiwon lafiya dake jinyar masu cutar sun fantsama cikin yajin aiki har sai gwamnati ta kara masu albashi sabili da hadarin da suke fuskanta.

Jami’an kiwon lafiya a Laberiya na haramar tafiya yajin aiki biyo bayan rashin jituwa da aka samu dasu dangane da kudaden da ake biyansu, lamarin da ka iya kawo mummunan tsaiko ga yaki da suke yi da cutar Ebola.

Dubban ma’aikatan kungiyar ayyukan kiwon lafiya ta kasa, ko Liberia’s National Health Workers Association a turance sunce baza su je aiki ba yau Litinin, sai in har an kara musu albashi saboda hadarin aikin da suke yi na jinyar jama’ar dake dauke da cutar Ebola.

Wadannan ma’akata sun nemi a yi musu karin albashi na dala $700 akan dala $200 ko $300 da ake biyansu kowani wata.

Kasar Laberiya itace kasar da tafi kowacce adadin mutanen da suka kamu kuma suka rasa rayukansu daga cutar Ebola, lamarin da ya raba mutane sama da 2,300 da rayukansu a kasar dake fama da talauci.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG