Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola Tana Yiwa Yammacin Afirka Barazana


Margaret Chan, shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO.
Margaret Chan, shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO.

Shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO a takaice tace cutar ebola na yiw a kasashen yammacin Afirka barazana

Shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya Dr. Margret Chan tace cutar Ebola tana barazana ga al’uma da gwamnatin kasashe da suke yammacin Afirka.

Darekta janar ta hukumar da ake kuma kira WHO a takaice, ta fada jiya Litinin cewa “bata taba ganin inda cutar da take yaduwa tayi barnar da zata iya wargaza kasa kamar yadda Ebola take yi ba”.

A cikin wata sanarwa ga taron kasa da kasa kan harkokin kiwon lafiya a Phillipines, Dr. Chan tayi gargadin cewa yawan wadanda cutar take kamawa yana karuwa ainun a kasashen Laberiya da Saliyo da Guinea, tace annobar ta nuna yadda sam “duniya bata kimtsa” tunkarar annobar kiwon lafiya wacce taki- ci- taki cinyewa ba.

Wasu jami’an Majalisar Dinkin Duniya ciki har da babban magatakardanta Ban ki-moon, sun sha yin irin wannan gargadi dangane da annobar cutar Ebola, wacce zuwa yanzu ta kashe fiyeda mutane dubu hudu a yammacin Afirka.

Jiya Litinin a Laberiya, galibin ma’aikatan kiwon lafiya sun yi biris da kiran su tafi yajin aiki da kungiyoyinsu suka yi, suka je aiki.

Ahalinda ake ciki kuma, hukumomin kiwon lafiya a Amurka sun shawarci asibitocin da suke kasar su sake nazarin matakan da suke dauka ta jinyar wadanda suka kamu da cutar Ebola, bayanda aka samu mace ta farko data kamu da cutar sakamakon jinyar wani mutumin laberiya da cutar ta kashe cikin makon jiya.

XS
SM
MD
LG