Ciyarda Mabarata aLokacin Bukukuwan Sallah a Najeriya

Wasu musulmi suke fidar ragon layya.

Kungiyoyi da daidaikun jama'a suna tallafawa nakasassu da abinci lokacin bukukuwan sallah.
Wannan hayaniya , wasu Musulmi ne kimanin su 200 suka taru a wani gida su na cin abincin babbar sallah da aka dafa da naman saniyar layya da wani Fasto Kirista ya kawo, wani Musulmi kuma ya yanka.

Illahirin wadanda ke cin abincin nakkasassu ne ko kuma 'ya'yan su. Suna zaune a wani gida dake can da nisa a wani wuri mai daben kasa da gwamnati ta ba su a Kaduna, a inda babu magudanun ruwa. Da ba don wannan walimar da aka shirya mu su ba, da a ranar sallar ma sun fita yawon bara kamar yadda suka yi kullum.

Addinin Islama ya bukaci masu sukuni su yanka dabbobi su yi layya ranar babbar sallah, kuma daga cikin naman su dauki sulusi daya a kalla, wato kashi daya cikin uku su rabawa miskinai. Daya daga cikin wadanda suka shirya walimar ita ce Maryam Abubakar, ta ce ranar sallah bai kamata kowa ya kwana da yunwa ba.

(( MURIYAR ABUBAKAR DA TURANCI))

“We want all these people to benefit from what we have. It’s a privilege. Instead of us to stay at home to eat what we have alone, no we decide, let us come and share with them. Let them rejoice with us.”

FASSARA: " Mu na so wadannnan mutane su amfana da abun da Allah Ya ba mu. Su ne marasa galihu. Maimakon mu zauna a gidajen mu mu cinye mu kadai, shi ya sa muka yanke shawarar cewa bari mu zo mu raba tare da su. Su ma su zo mu yi murna tare, mu ji dadi tare da su."

Sauran wadanda suka shirya walimar, sun yi ne ba don addinin su ya wajabta mu su yin hakan ranar babbar sallah ba, amma sun shiga an dama da su ne a wani kokarin neman kawo karshen rigingimun addini.

Fasto Yohanna Buru ya ce idan ana son hana faruwar rikici da tashin hankali tsakanin Musulmi da Kirista a yankin, hanya mafi dacewa ita ce shugabannin addinan biyu su hada hannu su yi ayyukan taimako tare.

((MURIYAR BURU DA TUTANCI)

“We want peace in northern Nigeria, in Nigeria, West Africa, Africa and the world entirely.”

SAHABO:" Mu na son wanzuwar zaman lafiya a arewacin Najeriya, da duka kasar Najeriya, da Yammacin Afirka, da Afirka, da ma duniya baki daya."

Rilwanu Mohammed Abubakar shi ne tsohon shugaban kungiyar nakkasassu ta Najeriya, ya ce duk da tsoron barkewar rikici ranar sallah, ciyar da miskinai a gidan su na hana afkuwar hadura kamar motoci su buge guragun da cutar polio ta nakkasa, wadanda ba su da kafafun yawo, sai da taimakon wata 'yar motar katako da suke yi.

((MURIYAR MOHAMMED ABUBAKAR DA TURANCI)

“Some of our members, most particularly the children, do have accidents as they normally go search for food when it is a celebration like this.”

FASSARA : " A lokutan sallah irin haka, wasu 'yan kungiyar mu, musamman ma yara su na haduwa da hadura idan su fita neman abinci kamar yadda suka saba."

Malam Rilwanu ya ce ciyar da nakkasassu a gidan su, ya na da na shi cikas saboda masu shirya irin wannan walima, kan kawo abincin da zai ishi mutum 200, wato yawan wadanda ke gidan, amma yadda akasarin jama'a ke fama da fatara da talauci a wannan gari, nakkasassu su ne mafiya talauci, amma idan aka kawo abincin sai a tarar da karin wasu mutane 400 su na zaune a gidan fiye da yadda wadanda suka shirya walimar suka zata. Amma sun ce badi za su kai abincin da zai ishi mutum dubu.

Your browser doesn’t support HTML5

Ciyarda Mabarata A Lokacin Bukukuwan Sallah A Najeriya -