Da yawa daga cikin wadanda suka tattauna da wakilinmu Hassan Umar Tambuwal, sun ce a shekarar da ta shige, farashin dabbobin bai yi tashi kamar na bana ba, domin ragunan da ake sayarwa Naira dubu 25 zuwa dubu 28 a bana, an saye su a kan naira dubu 18 a shekarar da ta shige.
Sai dai masu sayar da dabbobin sun ce rashin kasuwa ya tilasta musu rage kudaden dabbobin a kan yadda suka fara tallata su. Wani mai sayar da dabbobin yace daga cikin raguna fiye da 200 da ya taho da su, guda 30 kawai ya samu zarafin sayarwa ya zuwa yanzu. Dalili ke nan da ya sa suka fara karya musu kudade.
Ga cikakken bayani a tattaunawar da wakilin namu yayi da masu sayen dabbobin a garin Ibadan.