Maniyatta takwas aka dawo da su dalilin shiga kasar ta Saudiya da takardun visa na bogi. Har maniyattan sun kai Madina kafin jami'an hukumar shiga da fita na kasar suka bankado su. Ba tare da bata lokaci ba suka maida su cikin jirgin da ya kawo su. Maniyattan daga jihar Legas suke kuma jirgin yawo suka shigo. In ji wani jami'in hukumar alhazan Najeriya ya ce ba za'a ba wani maniyacci laifi ba domin biya zai yi a yi masa takarda sai dai idan yana da masaniya.Kamfanin da ya yi masu takardun shi ne za'a bincika.
Hukumar alhazia ta Najeriya ta ce ta kan tantance kafanoni kafin ta basu izinin neman ma maniyatta takardar tafiya Saudiya. Bisa ga abun da ya faru sai an gama hidimar hajji bayan an koma gida kana a kaddamar da bincike. Idan kamfanin da ya bada takardar bogi yana cikin wadanda suka ba izini zasu dakarat da shi, kuma za'a bi wasu hanyoyi a hukunta shi.
Yanzu dai wadannan maniyattan ba zasu sauke farilla ba wannan shekarar sai kuma ta badi idan Allah Ya kaimu kuma sun samu takardun shiga sahihai.
Ga karin bayani.