Wakilin VOA Hausa, Mahmud Ibrahim Kwari, yace limamai a wadannan masallatai sun gudanar da hudubobi masu ratsa zuciya a kan muhimmancin zaman lafiya da kaunar juna a tsakanin al'ummar duniya, musamman ma na Najeriya.
Sheikh Abubakar Jibrin, wanda ya jagoranci sallar eid a masallacin Eid na tsohuwar harabar Jami'ar Bayero ta Kano, yace duniyar Musulmi tana cikin wani hali na damuwa a saboda tarzomar da take faruwa a kasashen Musulmi dabam-dabam.
Ya danganta wannan al'amari da irin siyasar dake faruwa a cikin kasashen, musamman ma a Misra da Sham, yana mai fadin cewa komawa kan turb ata gari ce kawai zata iya maganin wannan abu.
Shi ma mai martaba sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, ya roki 'yan Najeriya da su kasance masu gaskiya da rikon amana. Wannan shi ne karon farko da sarkin ya bayyana tare da yin jawabi gaban jama'a tun komowarsa gida daga jinya a kasar waje kwanakin baya.
Al'ummar Kano kuma sun bayyana farin cikinsu ganin yadda aka gudanar da wadannan bukukuwa na Sallah cikin annashuwa da kwanciyar hankali.