Cin Hanci Da Rashawa Ga Jami'an Kasar Laberia

Dalar Amurka

Wata kungiyar kallon kurilla a Birtani mai suna Global Witness, sun saki wani rahoton daya bayyana cewa fiye da Dalar Amurka Dubu Dari Tara da Hamsin ne tare wasu kudaden ake zargin ana bada cin hancinsu ga wasu jami’an kasar Laberia.

Wanda yace wani kamfanin da yake zaune a Birtaniya ne na hakar ma’adanai ya bada cin hancin kudaden da suka hada har da Lauyansu dan kasar Laberia Varney Sherman. Kamar yadda rahoton da aka yiwa take da ‘MAYAUDARA’ ya nuna.

Tare da shadarar da ta biyo bayan taken mai cewa, Kamfanin STABLE na son samun ‘yancin kwangilar ma’aikatar Wologizi Iron da ke Ore. Sherman wanda shine shugaban jam’iyyar mai mulki ta Shugaba Ellen Johnson Sirleaf.

Sun ce ya fadawa kamfanin na Stable cewa, in dai har suna son kwangilar kamfanin na sarrafa karafan, to dole sai an bada cin hanci ga wasu manyan kasar Laberia. Manyan kudaden da aka biya, rahoton ya gano cewa an sa lakanin ne kawai a takardun biyan.

Inda aka rubuta an biya Bigboy 1 da Bigboy 2. Ma’ana babban yaro na daya da babban yaro na biya. Wani Jonathan Gant na kungiyar ta Global Witness yace, kungiyarsa na nan akan bakan rahotonta.