Rundunar Sojojin kasashe ma’abuta tafkin Chadi ta ce taron tsaro da kasashen su ka fara yau a babban birnin Tarayyar Najriya Abuja, zai yi tasiri sosai a yakin ta da ‘yan Boko Haram.
Wakilin Muryar Amurka a Abuja da ya turo wannan rahoton Hassan Maina Kaina, ya lura cewa wannan taron wani dori kan abubuwan da aka cimma taron da kasashen su ka yi a birnin Paris a baya, ciki har da batun yinkurin kwato ‘yan matan Chibok.
Kakakin Rundunar kasashe ma’abuta yankin na Chadi, Kanar Muhammed Dole ya gaya ma wakilinmu Hassan cewa ga dukkan alamu za a kara ba ma rundunar goyon baya a yakin da ta ke yi da Boko Haram. Haka zalika, hukumar raya yankin tafkin Chadi ta bukaci da a mai da hankali kan abubuwan da za su kawo farfadowa da kuma bunkasa yankin na Tafkin Chadi.
Ga wakilinmu Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton: