Jami’in bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Taraba, furfesa Mohammed Kyari, ya bayyana dalla-dallar sakamakon zaben gwamnan jihar Taraba, wanda dan tarakar gwamnan jam’iyyar DPD Mr. Darius Ishaku ya ce. Da yake bayyana sakamakon zaben da harshen Turanci, furfesa Kyari y ace, “Ni ne jami’in bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Taraba, wanda aka gudanar ranar 26 ga watan Afirilun shekara ta 2015. Ina mai cewa an gudanar da zaben kuma ‘yan takarar sun sami kuri’u kamar haka: A’isha Jummai Alhassan ta APC ta samu kuri’u 275984; Darius Dickson Ishaku na PDP ya samu 369318. Saboda haka, dayake Darius Dickson Ishaku na PDP ya cika sharadin da doka ta tanada ta wajen samun kuri’un da su ka fi yawa, an ayyana shi a matsayin wanda ya ci zaben.
Wakilinmu Sanusi Adamu ya bayyana cewa dan takarar na PDP ya yi galaba kan ‘yar takarar APC ne da jimlar rarar kuri’u 93, 344. Ya ce zababben gwamnan ya yi jawabi ga mutanen jihar, inda ya yaba da hakuri da kuma natsuwar da y ace sun nuna gabani da kuma bayan zaben, inda y ace zai fi mai da hankali wajen hadin kan mutanen jihar da kyautata sauran al’amura. Ya ruwaito shi ya na cewa, “To, abin da na lura shi ne, kamar dai komai ya rushe; mu fara da batun rashin zaman lafiya: Yanzu babu zaman lafiya; me za ka gina? Ko a wurina a kudancin Taraba kullum sai ko ka ji wannan ya yaki wannan, wannan ya yaki wancan. To rashin zaman lafiyan nan ne ba na so, kuma in Allah ya yadda zan kawo zaman lafiya na dindindin a jihar Taraba, kamar yadda aka sani a da, mu zauna da juna lafiya.”
Wakilin na mu ya kuma ruwaito wani dan jihar ta Taraba mai suna Alhassan Hamman na cewa sabon gwamnan zai fuskanci kalubalen da su ka hada da bukatar sanya mutanen jihar Taraba su kalli juna a matsayin ‘yan’uwa, wanda ya ce shi ne kalubale na farko.
To saidai wakilin na mu ya ce ‘yan sa’o’i bayan bayyana sakamakon zaben, sai ‘yar Tarakar jam’iyyar APC, Hajiya A’ishatu Jummai Alhassan ta kira taron ‘yan jaridu, inda ta shaw alwashin zuwa kotu saboda a cewarta, hukumar zabe da gwamnati mai ci sun hada baki wajen zaluntarta. Ta kara da cewa, “Na ce ban yadda da sakamakon zaben ba; kuma na ba da hujjoji na – na ba da hujjoji kamar haka: na daya, ba a yi amfani da “Card Readers” ba a wurare da yawa, na biyu an yi amfani da “card readers” din kuma aka yi magudi; na uku ba a kai kayan zabe ba a wasu wurare – ko nan da shekara goma zan rika fada Darius bai ci zabe ba, kuma su ‘yan PDP ma sun sani – bai ci zabe ba, bai ci zabe ba, bai ci zabe ba.”
Your browser doesn’t support HTML5