Fidelis ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi ta musamman da Sashen Hausa na Muryar Amurka inda ya ce har yanzu jam’iyyar ta PDP ta na nan da karfi har yanzu.
“Ni ban yadda da wannan ba, wannan ba zai taimaki kowa ba, wadannan ‘yan ci rani ne kawai, ba wai don jam’iyyar ka ba ta da kyau ba, sai ka gudu, zauna a wurin a gyara.” In ji Fidelis.
Tsohon gwamnan ya kuma kara da cewa har yanzu jam’iyyar ta PDP ta nan da karfin ta kamar yadda aka santa inda ya yi zargin cewa wadanda ke rike da jam’iyyar ne ba su san asalin matsalolin jam’iyyar ba.
Ya kuma ce akwai illa babba idan har aka bar Najeriya ta zama kasa mai jam’iyya guda domin akwai bukatar a dinga saka gwamnati a hanya.
“Ya kamata a samu abinda idan gwamnati ta yi a dinga gaya mata ko ta yi daidai ko ba ta yi dai dai ba, amma jam’iyya guda da ba za ta taimake mu ba.”
A lokacin da ya ke bayani kan irin adawar da PDP za ta yi, Fidelis ya ce, kafin nan akwai bukatar jam’iyyar ta PDP ta koma gida ta sake lale domin a ga inda aka yi kuskure saboda a gyara, yana mai cewa akwai kuma bukatar jam’iyyar ta koyi zama a bangaren adawa kamar yadda APC ta yi.
Game da siyasar jihar Filato, tsohon gwamnan ya ce, akwai bukatar a hada kan kowa da kowa saboda jihar ta koma yadda ta ke kamar yadda aka san ta.
“Muna so Filato ta dawo yadda ta ke kamar yadda, wato yadda kowa ya san Filato, duk za a hada hanu a samu a ci gaba.” Ya kara da cewa.