Cibiyar Habaka Binciken Rayuwar Bil Adam a Jami'ar Bayero

Jami’ar Bayero ta Kano ta kafa wata sabuwar Cibiya ta nazarin habaka bincike da bada horo kan al’amuran tattalin arziki, zamantakewa da kuma kimiyyar kididdigar Jama’a,

Cibiyar da hukumar gudanarwar Jami’ar ta amince da kafuwarta ta kunshi nazari da bincike a kusan dukan fannoni na rayuwanr bil Adam, wadanda suka hada da tattalin arziki da aiyukan noma da kiwon lafiyar jama’a, da zamantakewa da siyasa da kuma kimiyyar kididdigar jama’a.

Kwamitin da aka dorawa alhakin tsara yadda aiyukan cibiyar zasu gudana ya shirya taron masu ruwa da tsaki a harabar Jami’ar ta Bayero.

Farfesa Ismaila Zango, na sashen nazarin zamantakewar dan Adam, a jJami’ar, wanda shine shugaban kwamitin yace “Zai yi kyau kafin ace tafara aiki a tattaro masana daga bangarori daban daban da kuma wadanda suka jibaci harkokin wadannan abubuwan suma su zo su ga shin wana irin abu suke gani yakamata cibiyar ta maida hankali akai .”