Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaman Gida ya Kare ga Daliban Tsangayar Shari'a ta Aminu Kano


Tsangayar Malam Aminu Kano
Tsangayar Malam Aminu Kano

Ilimi a yankin jihohin Arewa na cigaba da fuskantar matsaloli da dama, duk da kasancewar gwamnatoci na ta ikirarin kashe makudan kudade don kyautata tsarin. Amma har a zuwa yanzu anasamu wasu matsaloli da suke gurgunta cigaban da bangaren ilimi yakamata ace ya samu. Ana cikin haka sai ga daliban tsangayar koyar da ilimin Shari’a ta Malam Aminu Kano, da ke Kano, na korafi dangane da halin da sukeciki a yanzu, tun kimanin watanni shida da suka gabata suka kamala karatunsu, na zangon farko amma har zuwa yanzu babu wani labara dangane da komawarsu makaranta, sun kuma kokarta wajen gano menene dalilin da yasa hakan ta kasance, amma ba wani labara dangane da hakan. A bangare daya kuwa sun samu labarin cewar gwamnati bata biya kudin makarantarsu bane shiyasa haryanzu ba’a basu damar komawaba.

A zantawa da mukayi da shugaban makarantar Dr. Garba Shehu, yayi muna karin bayani dacewar, dalilin da yasa basu bama daliban damar dawowa makaranta ba shine, akwai karancin azuzuwa, da na malamai da zasu koyar da daliban a lokaci daya.

Domin kuwa yanzu makarantar tana da bangare biyu, da na karatun dipiloma a fannin shari'a da na masu koyon karatun malinta, wanda a sanadiyar samun chanji da akayi a fannin ilimin makarantun firamari, a kasar yasa suma basa samun aika dalibai masu koyon karatu sana’ar koyarwa a makarantun firamari. Amma suna koakarin su don ganin dalibai 'yan NCE 1,2,3 sun dawo makaranta a karshen wanna watan.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG