Kasar Sin ta sanar da sanya takunkumai da ba kasafai aka saba gani ba a kan wasu kamfanonin tsaron Amurka biyu, saboda abin da ta ce na goyon bayan sayar wa Taiwan makamai.
WASHINGTON, D. C. - Beijing ta yi ikirarin tsibirin mai cin gashin kansa da ke bin tafarkin dimikuradiyya a matsayin yankinta da za’a karbo da karfi idan ya kama. Sanarwar ta hana taba kadarorin kamfanonin ayyukan soji da suka shafi jiragen sama da kuna na doron kasa da ke a cikin kasar Sin.
Har ila yau, ta haramtawa mahukuntan kamfaninin shiga kasar. Takardun bayani sun nuna kamafanin General Dynamics yana aiki da rabin dozin na kamfanin Gulfstream da ke ayyukan sabis na jiragen sama a Sin.