Kasar Amurka na da niyyar daukar mataki dangane da cin zarafin bil adama da ake yi a Xinjiang, da ke China. Dalilin haka ne, Tarayyar Turai, Birtaniyya, Canada, da Amurka suka sanar da hadin kai dan sanya takunkumi kan jami’an China dangane da mummunan cin zarafin bil adama da ke faruwa a Xinjiang.
Cin zarafin da China ta yi a Xinjiang sun hada da tsare mutane da yawa a sansanonin horo, da tilasta masu yin aiki, da hana haihuwa, da tsananin takurawa kan ‘yancin yin addini ko imani, da kuma takurawa mai tsanani kan yadda ‘yan Uyghurs ke amfani da harsunansa da ma al'adunsu.
“Yayin da kasashen duniya ke ci gaba da Allah wadai, China na ci gaba da aikata kisan kare dangi da aikata laifuka kan 'bil Adama a Xinjiang, "in ji Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken a cikin wata sanarwa da ya rubuto. “Amurka ta sake nanata kiran da ta yi wa China don ta kawo karshen danniyar hakin yan Uyghurs, wadanda galibinsu Musulmi ne, da mambobin wasu kabilu da ma wasu kananan addinai marasa rinjaye a Xinjiang, gami da sake duk wadanda aka tsare ba bisa son rai ba a sansanoni da wuraren tsare mutane. ”
A karkashin wani shiri na sanya takunkumi da ake kira Global Magnitsky sanctions program, Amurka ta ambaci wasu jami'an China biyu" dangane da mummunar cin China a Xinjiang," Sakatare Blinken ya rubuta. Jami'an su ne Wang Junzheng, sakataren kwamitin jam'iyyar na kamfanin samar da kayayyakin gine-gine na Xinjiang, da Chen Mingguo, Daraktan Ofishin Tsaron Jama'a na Xinjiang. Takunkumin na nufin cewa duk wata dukiyar wadannan mutane da suke ciki ko suka shigo Amurka an dakatar da su, kuma Amurkawa ba zasu iya mu'amala da su ba.
Wannan matakin da Amurkan ta ɗauka an yi shi ne cikin haɗin kai ga ayyukan abokan ƙawancen ta a Tarayyar Turai, Birtaniyya da Canada, waɗanda su ma suka sanya takunkumi kan jami'ai biyu da sauransu.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa, ministocin harkokin wajen Burtaniya, Canada, da Amurka sun ce matakan da suka hada kai, daidai suke da matakan da Tarayyar Turai ta dauka, "sun aike da sako bayyananne game da take hakkin bil adama da cin zarafinsu a Xinjiang." Sun yi kira ga China da ta dakatar da ayyukanta na danniya da kuma barin masu bincike masu zaman kansu daga Majalisar Dinkin Duniya da ma na 'yan jarida da jami'an diflomasiyyar kasashen waje samun dama cikin yankin ba tare da cikas.
Ministocin harkokin wajen sun bayyana cewa, "Za mu ci gaba da hada kai tare, don haskaka take hakkin bil Adam da China ke yi." "Mun tsaya a dunkule kuma muna kiraa yi adalci ga wadanda ke cikin wahala a Xinjiang."