Tsohon Sakataran Harkokin Wajan Amurka Mike Pompeo, na daga cikin mutane 28 da Ma’aikatar Harkokin Wajan China ta ce sun shirya da kuma aiwatar da wasu jerin matakai marasa dadi, wanda suka shafi harkokin cikin gida na China, suka kuma yi katsalanda kan muradun China, da bakantawa jama'ar kasar China da kuma lalata danganta tsakanin Amurka da China.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajan China Hua Chunying ta bayyana Pompeo a matsayin “sauna” a lokacin da ta ke ganawa da manema labarai yau Alhamis a Beijing.
China ta kuma kakaba takunkumi kan tsohon mai bawa shugaba Donald Trump Shawara kan kasuwanci, Peter Navarro, da tsohon mai bada shawar kan tsaron kasa Robert O’Brient, da kuma wanda O’Brient ya gada, John Bolton.
Ma’aikatar Harkokin Wajan ta ce takunkumin da aka sakawa daidaikun da kuma iyalansu shi ne “an haramta musu shiga China, Yankin Hong Kong, da kuma Macao.
Hakannan kuma ta ce an haramta musu da kamfanonin da suke da alaka da su daga yin kasuwanci da China.