Bankin CBN Ya Kara Yawan Kudin Ruwa Zuwa Kaso 18 Cikin 100 Daga Kaso 17.5

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

Shugaban babban bankin Najeriya wato CBN ya bayyana cewa, kwamitin manufofin kudin bankin ya kada kuri’ar kara yawan kudin ruwa da maki 50 zuwa kaso 18 cikin 100 daga kaso 17 da digo 5 cikin 100.

Wannan mataki dai an dauke shi ne don dakile hauhawar farashin kayayyaki a halin yanzu da ya kai kaso 21 cikin dari kuma saboda a saukaka wa ‘yan kasa da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar.

Gwamnan bankin CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana matsayar da kwamitin manufofin bankin ya cimma bayan taronsu na yini biyu wanda mambobi 10 suka amince da daga kudin ruwan daga kaso 17 da digo 5 cikin 100 zuwa kaso 18 wanda ke nufin an sami karin maki 50 a kan yadda yake a da a ranar Talata yayin da yake karanta sanarwar taron MPC karo na biyu na shekarar 2023 a birnin tarayya Abuja.

Godwin Emefiele Da Mambobin Kwamitin NPC

Malam Haruna Bala Mustapha shi ne daraktan lura da harkokin bankuna na babban bankin CBN a Najeriya, ya ce taron kwamitin manufofin kudi da aka kammala a ranar Talata ya duba muhimman abubuwa ciki da matsalar hauhawar farashi da ya addabi kasar don kawo sauki da kuma irin tasirin da rushewar wasu bankunan kasar Amurka za su iya yi a Najeriya.

Sai dai, a nasa bangare, masanin tattalin arziki a Najeriya, Mal. Yusha’u Aliyu ya ce matakin na kwamitin manufofin kudi na bankin CBN zai kara hauhawar farashi ne kawai, yana mai cewa ana yin irin wannan karin ne don rage yawan kudi da ke yawo tsakanin al’umma, wanda bankin ya riga ya janye kudaden daga hannun al’umma.

Mambobin Kwmaitin NPC

Baya ga batun kara kudin ruwa, Emefiele ya bayyana cewa bankin ya goyi bayan hukuncin kotun koli na a ci gaba da mu’amala da tsoffin takardun kudi baya ga sabbin da aka sake fasalinsu wanda adadinsu ya kai kusan Naira tiriliyan daya.

Kazalika, Emefiele ya ce babban bankin kasar na da kwarin gwiwa a kan bankunan kasuwancin Najeriya wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ganin yadda suke ci gaba da jure wa asalin jarin da suka zuba na kaso 13 cikin 100, ba da lamuni wanda mutumin da ya karbin rance bai sanya lokacin fara biyansu ba na kaso 4.2 cikin 100 da kuma kudaden ajiyar bankunan da aka kara zuwa naira tiriliyan goma sha hudu.

Saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

Your browser doesn’t support HTML5

CBN Ya Kara Yawan Kudin Ruwa Zuwa Kaso 18 Cikin 100 Daga Kaso 17.5.mp3