ABUJA, NIGERIA - Mai shari’a Emmanuel Agim ne ya karanta hukuncin kotun kolin da ya baiwa ‘yan Najeriya damar ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudin na naira 200, 500 da ma dubu 1 a ranar Juma’a, 3 ga watan Maris da muke ciki inda kotun ta yi watsi da bukatar da Antoni Janar na Tarayya, da na jihohin Bayelsa da Edo suka shigar tun farkon shari’ar, na cewa kotun kolin ba ta da hurumin sauraron karar, inda mai shari’a Agim yace suna da hurumi.
Kotun kolin ta kuma soki lamirin manufofin gwamnatin tarayya na sauya fasalin takardun kudin Naira, inda ta bayyana matakin a matsayin yin karan tsaye ne ga kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 kamar yadda aka yi masa gyaran fuska.
Kotun ta yi la’akari da sashe na 23 sakin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin kasar da ya ce dole ne takaddamar da ke tsakanin Gwamnatin Tarayya da Jihohi ta kunshi doka ko kuma ta gaskiya.
Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana jin dadinsa a game da hukuncin kotun yana mai yiwa alkalai da suka zartar da shi godiya a kan yadda suka saurari koken talakawa.
Aminu Junaidu, shi ne kwamishinan shari'a na jihar Zamfara, ya ce hukuncin kotun na nufin cewa ‘yan Najeriya na da damar ci gaba da yin amfani da tsoffin takardun kudin na naira 200, 500 da ma dubu daya zuwa nan da sama da watanni 9 masu zuwa.
Kanu Agabi mai mukamin SAN shi ne lauyan da ya kare wadanda ake kara a gaban kotu, wato gwamnatin tarayya, babban bankin CBN da antoni janar na tarayyar kasar, inda ya ce dole ne wadanda ake kara su bi umarnin kotun kolin don mutunta dokar kasa.
Malama Rukayya, wata 'yan Najeriya mai sana'ar sayar da fura da Nono a cikin harabar kotun kolin, ta ce hakika sabon tsarin canjin kudin ya kuntatawa talakawa kuma ta ji dadi da kotun ta ji kokensu ganin yadda suka shiga halin matsin rayuwa bayan matakin na gwamnatin tarayya.
Jihohi 16 karkashin jagorancin Kaduna, Kogi da Zamfara ne suka shigar da kara a gaban kotun kolin da ta soke manufofin kudin na gwamnatin tarayya da kotun tace yana kuntata wa ‘yan Najeriya da ba su ji ba ba su gani ba.
Duk kokarin jin ta bakin gwamanatin tarayya, ko bankin CBN da Antoni Janar a yayin hada wannan rahoton dai ya ci tura.
Saurari cikakken rahoto daga Halima Abdulrauf: