Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rawar Da Buhari Zai Iya Takawa Wajen Ci gaba Da Amfani Da Tsofaffin Takardun Naira


Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

Har yanzu wasu 'yan Najeriya na dari-dari wajen karbar tsofaffin takardun kudin Najeriya (Naira) sama da kwanaki goma bayan umurnin babban bankin kasar CBN na tabbatar da hallarcin kudaden bisa umarnin kotun koli.

Kwana daya bayan da Babban Bankin Najeriya ta bada umarnin cigaba da anfani da kudaden Naira 200 da 500 da 1000, Jama'a naci gaba da dariri da umarnin. Abunda masana tattalin arziki sukace zai dauki lokaci. Wakilinmu na Lwgasa Babangida Jibrin yaji ta bakin wasu kananan yan kasuwa.

A wata sanarwar da ya fitar a jiya Litinin, mai Magana da yawun bakin babban bankin Najeriyan CBN Isa Abdulmumin, ya nanata cewa har yanzu tsofaffin takardun kudin sun hallarta har ranar 31 ga watan Disamban bana.

Kafin gwamnatin tarayyar Najeriya da babban bankin kasar su bayyana matsayarsu, ‘yan Najeriya da dama sun shiga halin ni ‘yasu wajen samun takardun naira inda wasu suka mutu sakamakon wahalar takardun kusin nairan.

Yayin da 'yan Najeriya suke cigaba da bayyana ra’ayinsu, wakilin Muryar Amurka Babangida Jibrin ya tattauna da wasu a birnin Lagos inda Shehu Dan Nufawa wani mai sana’ar saida nama y ace y afara karbar kudin domin gudun abun da ka iya zuwa ya dawo kasancewar umarnin babban bankin Najeriya kawai suka ji amma har yanzu basu ji daga bakin shugaban kasa ba.

Shi kuma Zakariya’u wanda yake harkar kasuwanci ya ce har yanzu ba su fara karbar kudin ba domin sun karba sun amma da suka kaiwa manyansu sun kin karbar kudin, ya kuma kara da cewa kwanakin baya ya kai tsoffafin kudin banki amma suka ce da shi “on your own” wato abun nufi, can ta matse maka- inda suka ce said ai ya kai CBN. Yace a dalilin haka bazasu fara karba sai har sai shugaba Buhari ya tabbatar.

Shi kuma Muhammadu Sunusi ya shedawa wakilin Muryar Amurka cewa “yanzunnan ina zuwa mai na ya kare, sai na shiga wani gidan mai kusa da ni amma suka ce su basu fara amsa ba domin suna jiran shugaban kasa ya furta da kansa.

Duk da cewa tuni shugaba Muhammadu Buhari ya nesanta kansa game da kin bin umarnin kotun koli da ta zartar fiye da kwanaki goma da suka gabata, alamu na nuni cewa ‘yan Najeriya za su fi samun natsuwa su karbi kudin idan ya fito ya yi wa al’ummar kasar jawabi.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG