A daidai lokacin da hauhawar farashin kayayyaki ke kara kamari, Babban Bankin Najeriya wato CBN ya kara kudin ruwa da maki 150 daga 24 da digo 75 zuwa Kaso 26 da digo 25 lamarin da tuni masana tattalin arziki suka ce zai kara jefa kananan yan kasuwa cikin tsanani, wasu kuma na cewa matakin da aka dauka ya dace.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ne ya bayyana daukan wannan matakin jim kadan bayan kamalla taron manufofin kudi na yini biyu a yau Talata inda aka kara kudin ruwa da maki 150 kuma a yanzu yake kan kaso 26 da digo 25.
Jagora a fannin sadarwa da hulda da jama’a na bankin CBN, Dakta Ladi Raulatu Bala-Keffi ta yi karin bayani a kan matakin na CBN ta na mai cewa an dauki matakin kara kudin ruwa ne don daidaita al’amura a kasar.
Tuni dai ‘yan Najeriya suka fara tofa albarkacin bakin su a game da matakin na CBN inda mai fashin baki a kan al’amurran yau da kullum, Mallam Bello Ibrahim ya ce bankin CBN na son tsayar da ayyuka cak.
Saidai masanin tattalin arziki, Mallam Kasim Garba Kurfi ya ce matakin da bankin CBN ya dauka ya dace saboda idan ba’a yi hakan ba mutane ke daukan kudi zuwa sayen kaya a kasuwanni farashin kayayyaki kuma su ci gaba da tashi.
A yanzu dai alkaluman kididdiga sun yi nuni da cewa masu kanana da matsakaitan sana’o’i na ci gaba da fama da matsi a yanayin tafi da kasuwancin su na yau da kullum ganin yadda ake shigowa da akasarin kayayyakin amfani lamarin da masana tattalin arziki ke cewa idan ba’a sauya salo ba, nan gaba kadan za’a iya fuskantan rugujewar tattalin arzikin kasar baki daya.
A saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5