Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Farashin Kayan Masarufi Ke Ci gaba Da Tashi A Najeriya – Cardoso


Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso (Hoto: Facebook/CBN)
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso (Hoto: Facebook/CBN)

Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Olayemi Cardoso ya ce kayayyakin abincin da gwamnati take saya don rabawa mabukata na daga cikin dalilan da suke kara hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

Cardoso ya bayyana hakan ne a yayin wani taron kwamitin da ke bibiyar tsare-tsare hadahadar kudade, wanda aka wallafa rahoton wtan Maris a shafin babban bankin na CBN a ranar Litinin a cewar gidan talabijin na Channels.

A taron ne kwamitin ya kara adadin kudin ruwa daga 22.75 zuwa 24.75, matakin da kwamitin ya ce ya dauka don karya tagomashin matsalar hauhawar farashin na kayayyaki.

Sai dai tsarin yadda mutane ke sayen kayayyaki da Hukumar Kididdiga ta Nigerian Bureau of Statistics ta fitar (NBS) a watan Afrilu, ya nuna cewa matsalar hauhawar farashin kayayyakin ta karu zuwa kashi 33.2 a watan Maris.

Tashin farashin kayan masarufi ya kai kashi 40.01, inda yakan karu a kowace shekara zuwa 15.56 daga kashi 24.45 watan Maris din 2023.

Cardoso ya kara da cewa, duk da matakan da aka dauka don magance matsalar ta hauhawar farashin kayayyakin lamarin ya ki sauyawa duk da daidaito da aka samu a farashin canjin kudaden waje.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG