CBN Ya Gargadi Bankuna, Masu PoS Kan Matsalar Karancin Takardun Naira

Banban Bankin Najeriya, CBN

Babban bankin ya ce yana gudanar da bincike bayan samun rahotannin da ke zargin bankunan kasar da hada kai da masu PoS wajen haifar da matsalar karancin naira, lamarin da ya ce yana shafar tattalin arzikin kasar.

Babban Bankin Najeriya CBN ya gargadi bankunan kasar da masu hadahadar kudade ta na’urar PoS wajen hada kai wanda hakan ke kara ta’azzara matsalar karancin takardun naira da ake fuskanta a wasu sassan kasar.

Cikin wata sanarwa da bankin na CBN ya fitar kamar yadda Channel TV ya ruwaito, kakakin bankin Sidi Ali Hakama ya ce hadin kan bangarorin biyu zai kara haifar da matsalar wanzuwar takardun naira a kasar.

Tun bayan da gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ta yi wa wasu takardun naira garanbawul a bara, aka yi ta fuskantar matsalar rashin takardun naira a hannun jama’a.

Ko da yake, daga baya an shawo kan matsalar, amma a ‘yan makonnin bayan nan matsalar ta sake kunno ki.

Babban bankin ya ce yana gudanar da bincike bayan samun rahotannin da ke zargin bankunan kasar da hada kai da masu PoS wajen haifar da matsalar karancin naira, lamarin da ya ce yana shafar tattalin arzikin kasar.

“Bankin CBN ba zai lamunci wannan ta’asar ba, kuma yana kan gudanar da binciken korafe-korafen da ake samu, wadanda za su iya yin mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasa.

“Saboda haka, CBN na gargadi ga bankuna da masu PoS da su guji wannan dabi’a, domin za a hukunta duk wanda aka samu hannunsa a ciki.” Sanarwar ta ce.

A watan Oktoban 2022, babban bankin na CBN ya sanar da sauya fasalin takardun kudaden 200, 500 da kuma 1,000.