BAUCHI, NIGERIA - Sai dai kuma hukumar kula da bankuna da sanya ido da kuma bada kariya ta hanyar Inshora da ake kira Nigeria Deposit Insurance Corporation NDIC, ta ce ta biya biliyoyin Naira ga mutanen da kudadensu su ka makale sanadiyyar rufe bankunan.
Amini Hamisu, mataimakin manajan hukumar NDIC na shiyyar Bauchi, a tattunawar Muryar Amurka da shi ya fayyace mana irin bankunan da rufewar ta shafa.
Ganin cewa, a jiya ne aka kaddamar da bukin ranar ajiya a bankin a Duniya domin wayar da kan jama’a da kuma gabatar da kasidu a wuraren da aka gudanar da tarurruka don fadakar da mutane muhimmancin yin ajiya a bankin, mun ji daga Ajiya Bah Zarma, konturola na hukumar NDIC dake shiyyar Bauchi, akan ko ‘yan Najeriya suna da azamar yin ajiya a bankin.
A daya gefen kuma mun ji tabakin wassu ‘yan Najeriya kan batun ajiyar kudi a bankuna, da ra’ayoyinsu game da rufe bankunan.
Taken ranar yin ajiya a bankin na wannan shekarar, shi ne ka nemi galaba akan yau dinka domin raya gobe.
Saurari cikakken rahoto daga Abdulwahab Muhammad:
Dandalin Mu Tattauna