A sanarwar, mai ɗauke da sa hannun Daraktan sadarwar Bankin, Isa Abdul-Mumin, ya ce Babban Bankin na Najeriya CBN, zai ci gaba da amsar tsoffin kuɗaɗen, kuma izuwa yanzu ba ta sanya ranar daina amfani da tsoffin kuɗaɗen ba.
Idan za a iya tunawa, babban Bankin na CBN, ƙarƙashin tsohon Gwamnan Bankin Godwin Emeifele ta buga sabbin kuɗaɗen Naira 200, 500 da kuma 1,000, kuma ta sanyawa tsofaffin kuɗaɗen wa'adin daina amfani dasu a watan Disambar 2023.
Sai dai kafin wannan sanarwa ta babban Bankin Najeriya, ƴan ƙasar sun fuskanci ƙarancin kuɗaɗe a hannuwansu da zasu gudanar da rayuwar yau da kullum.
Shin ko wannan sanarwa za ta iya kawo ƙarshen ƙarancin kuɗaɗe da al'ummar ƙasar ke kokawa, tambayar da wakiliyar Sashin Hausa ta yi wa Dakta Isa Abdullahi Kashere, manazarci kuma malami a jami'ar Tarayya ta Kashere dake Jihar Gombe kenan, ga kuma ƙarin bayani da ya yi.
"Dakatar da amfani da tsoffin kuɗaɗen na Naira 200, 500 da kuma 1,000 tsari ne na tsohuwar Gwamnati, sai dai zuwan wannan gwamnati, ta yi fatali da wancan tsari inda tace a cigaba da amfani da tsoffin kuɗaɗen, ƙwarai wannan zai taimaka wajen rage zafin raɗaɗin ƙarancin kuɗaɗen a hannun mutane, kuma abu ne me kyau".
A hirarsa da Muryar Amurka, ɗaya daga cikin ma'aikatan Bankunan Najeriya da baiso a ambaci sunansa ba, ya ce "su bankunan ƙasar kansu na fama da ƙarancin takardun kuɗaɗe, domin yanzu ba'a cika kawo ajiyar kuɗaɗe ba, amma wannan sanarwar zata iya taimakawa wajen sauƙaƙa hada-hadar kuɗaɗen".
Ƴan Najeriya dai na ganin wannan sanarwa ta CBN ka iya taimakawa wajen rage raɗaɗin ƙarancin kuɗaɗe a hannu da al'ummar ƙasar ke fama dashi.
Yanzu dai ƴan ƙasar na dakon ganin yadda babban Bankin na Najeriya zai wadatar da ƙasar da kuɗaɗen da suke buƙata a hannu.
Saurari rahoton Ruƙaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna