Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Ake Samun Karancin Takardun Naira A Wasu Bankunan Najeriya


Babban bankin Najeriya CBN
Babban bankin Najeriya CBN

“Yayin da muka farga da damuwar da jama’a ke nuna wa ta karancin kudade, muna so mu sanar da jama’a cewa akwai wadatattun takardun kudaden da za a gudanar da harkokin kasuwanci a kasar.

Babban Bankin Najeriya CBN, ya ce yana da wadatattun takardun kudaden naira yayin da ake samun rahotannin karancin kudade a na’urorin cire kudi na ATM da ma cikin bankuna a wasu yankunan kasar.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, babban bankin ya ce binciken da ya gudanar ya nuna cewa sanadiyyar cire kudade da bankuna suka yi daga babban bankin da kuma rububin da mutane suke yi na cire kudadensu a na’urorin ATM ne ya sa ake ganin karanci takardun kudaden.

“Yayin da muka farga da damuwar da jama’a ke nuna wa ta karancin kudade, muna so mu sanar da jama’a cewa akwai wadatattun takardun kudaden da za a gudanar da harkokin kasuwanci a kasar.

“Rassan babban bankin da ke jihohi na aiki domin tabbatar da cewa an samu yawaitar kudaden na takardu a jihohinsu.” CBN ya ce cikin sanarwar da ya fitar dauke da sa hannun Darektan Yada Labarai Isa AbdulMumin.

Bankin na CBN ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina rububin zuwa cire kudadensu cikin fargaba domin akwai kudi a kasa.

“Muna kuma ba ‘yan Najeriya shawara da su rika bin sauran hanyoyin biyan kudade wanda hakan zai rage dogaro da ake yi da tsurar kudi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG