"Canji Ba Zai Samu Cikin Sauri Ba" - Sabon Firai Ministan Birtaniya

  • Murtala Sanyinna
A wani jawabi da zai gabatar a ranar Talata, Starmer zai bayyana cewa "sauyi ba zai faru cikin dare daya ba" amma gwamnatinsa ta kuduri aniyar magance dimbin matsalolin da suka hada da cunkoson gidajen yari, har ya zuwa dogon jira da ake samu a sha’anin kiwon lafiya.

Firayim Ministan Birtaniya Keir Starmer zai yi jawabi ga 'yan kasar a mako mai zuwa kan cewa sauye-sauyen da ake bukata don gyara matsalolin Birtaniya za su dauki lokaci, yana mai cewa "al'amura za su kara tabarbarewa kafin mu sami sauki" a wani jawabi da ya bayyana a matsayin wata dama ta daidaicewa da al’umma.

Bayan zabensa a matsayin firaminista a watan Yuli, Starmer ya sha zargin tsohuwar gwamnatin ‘yan mazan jiya da barin Birtaniyya a cikin mawuyacin hali, lamarin da ya ce ya baiwa tsageru damar tada tarzomar kyamar baki a watan nan.

A wani jawabi da zai gabatar a ranar Talata, mako guda gabanin dawowar majalisar dokokin Burtaniya bakin aiki bayan hutun bazara, Starmer zai bayyana cewa "sauyi ba zai faru cikin dare daya ba" amma gwamnatinsa ta kuduri aniyar magance dimbin matsalolin da suka hada da cunkoso gidajen yari, har ya zuwa jira na zuwa dogon lokaci a sha’anin kiwon lafiya.

An tilastawa Starmer, tsohon darektan gabatar da kara, soke hutun sa na bazara a wannan watan, domin fuskantar tarzoma da ake kai wa musulmi da bakin haure hare-hare.

Rikicin ya faro ne bayan kisan wasu 'yan mata uku da aka yi a arewacin Ingila da bisa kuskure aka zargi wani dan gudun hijira mai kishin Islama bisa bayanan karya a shafukan sadarwa na yanar gizo.