Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Sandan Jamus Na Neman Wani Da Ya Kashe Mutum Uku Da Wuka Ruwa A Jallo


Yan Sandan Jamus na gudanar da bincike a wurin da wani mutum ya kai hari da wuka ya kashe mutum uku.
Yan Sandan Jamus na gudanar da bincike a wurin da wani mutum ya kai hari da wuka ya kashe mutum uku.

Jami'an 'yan sanda na musamman sun shiga aikin farautar wani mutum da ba a san ko su wanene ba, wanda ya kai hari da wuka a wani wajen taron jama'a a birnin Solingen da ke yammacin Jamus, inda ya kashe mutane uku tare da jikkata wasu akalla takwas, biyar daga cikinsu sun sami munanan raunuka.

A wata sanarwa da ‘yan sandan suka fitar ta ce, “A yanzu haka ‘yan sanda na gudanar da bincike mai zurfi domin neman wanda ya aikata laifin.” “A halin yanzu ana tambayar wadanda abin ya shafa da kuma shaidu,” in ji su.

‘Yan sandan dai ba su nuna cewa har yanzu sun gano maharin ba, tare da gargadin mutane da su yi taka tsantsan duk da cewa masu kakoki sun fara ajiye furanni a wurin. 'Yan sanda sun samar da wani shafin hanyar yanar gizo, inda shaidu za su iya loda hotuna da duk wani bayani da ya shafi harin.

Mutane sun sanar da ‘yan sanda jim kadan bayan karfe 9:30 na dare. Ranar Juma'a ga wani maharin da ba a san ko wanene ba ya raunata mutane da dama da wuka a tsakiyar dandalin, Fronhof. ‘Yan sandan sun ce sun yi imanin wani maharin shi kadai ne ya kai harin, kuma ba su bayar da wani bayani game da sunayen wadanda aka kashe ba.

“A daren jiya zukatanmu sun sosu. Mu a Solingen muna cike da firgici da bakin ciki. Abin da ya faru jiya a garinmu da kyar ya bar wani daga cikinmu ya yi barci,” magajin garin Solingen, Tim Kurzbach, ya ce, yayin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar, a kusa da wurin da aka kai harin.

“Bikin Al’adu,” wanda ke nuna bikin cika shekaru 650 na birnin, ya fara ranar Juma'a kuma ya kamata ya gudana har zuwa Lahadi, tare shagulgula masu yawa a tsakiyar tituna, suna ba da abubuwan jan hankali da nishadi kamar kide-kide da raye-raye.

An kai harin ne a cikin jama'ar da ke gaban mataki daya. Sa'o'i kadan bayan harin, fitulun wajen bikin na kunne yayin da 'yan sanda da masu bincike na binciken laifuka ke gudanar da ayyukansu.

Daya daga cikin wadanda suka shirya bikin, Philipp Müller, ya bayyana a kan dandalin a ranar Juma’a kuma ya bukaci mahalarta bikin da su “tafi cikin nutsuwa; tare da bude idanunsu, domin abin takaici ba a kama wanda ya aikata laifin ba.” Garin Solingen yana da mazauna kusan 160,000 kuma yana kusa da manyan biranen Cologne da Duesseldorf.

An soke sauran bukukuwan.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG