Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-Zangar Nuna Kin Jinin Tsarin Zabe A Indonisiya


INDONESIA-POLITICS/PROTEST
INDONESIA-POLITICS/PROTEST

Masu zanga-zangar na nuna bacin ransu kan yunkurin da 'yan majalisar dokokin kasar da abokan shugaba Joko Widodo suke yi na neman sauya tsarin zabe ta yadda zai amfane su.

Dubun dubatar mutane sun gudanar da zanga-zanga a birane da dama na kasar Indonesia a ranar Juma'a, suna masu matsin lamba ga hukumar zaben kasar da ta fitar da ka'idojin zaben yankuna, a daidai lokacin da suke nuna bacin ransu kan yunkurin da 'yan majalisar dokokin kasar da abokan shugaba Joko Widodo suke yi na neman sauya tsarin zabe ta yadda zai amfane su.

Zanga-zangar ta biyo bayan wata ranar da aka yi zanga-zanga inda aka tsare mutane 301, aka kuma yi amfani da hayaki mai sa hawaye da ruwan zafi wajen tarwatsa gungun mutanen da ke zanga-zangar a wajen majalisar dokoki, wadda a ranar Alhamis ta yi watsi da shirinta mai cike da ce-ce-ku-ce na yin kwaskwarima ga dokokin cancantar 'yan takara, bisa hujjar rashin amincewar mafi rinjayen ‘yan majalisar.

Zanga-zangar ta kasance tare da nuna fushi kan Jokowi a shafukan sada zumunta, wanda ya yi tsayin daka kan yin sauye-sauyen da aka tsara wanda zai ba dansa damar neman mukami a Java ta tsakiya, tare da hana wani babban mai sukar gwamnati yin takarar babban mukami na gwamnan Jakarta.

Da aka tambaye shi game da zanga-zangar, Jokowi ya ce yana da kyau mutane su bayyana ra’ayoyinsu.

Zanga-zangar dai ta dauki tsawon mako guda a fuskar siyasa, inda aka yi ta nuna bacin rai kan abin da masu sukar Jokowi ke bayyanawa da wani yunkuri na kara wanzar da karfin ikonsa, a daidai lokacin da ya ke share fage ga wanda yake son ya gaje shi, Prabowo Subianto a watan Oktoba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG