Masu shigar da kara a Venezuela sun gayyaci dan takarar jam’iyyar adawa Edmundo Gonzalez Urrutia, domin amsa tambayoyi a gobe Litinin, a wani sashe na binciken laifukan da suka biyo bayan zaben shugaban kasar mai cike da cece-kuce, da dan takara Nicolas Maduro ya yi iƙirari.
Babban Lauyan gwamnati, Janar Tarek William Saab, abokin Maduro, ya yi hasashe gayyatar a ranar Juma'a, sa’adda ya ke cewa Gonzalez Urrutia zai yi bayani kan "rashin biyayyarsa" ga hukumomi.
Saab ya ce shafin yanar gizo na 'yan adawa, inda aka wallafa cikakken sakamakon zaben, ya yi karan tsaye ga hurumin Hukumar Zaben kasar da ke da alaka da Maduro.
Hukumar ta CNE ta ayyana Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben na ranar 28 ga watan Yuli da kashi 52% na kuri'un da aka kada, amma ta ki fitar da cikakken sakamako, tana mai cewa masu kutse sun gurbata bayanan.
Wata tawagar sa ido daga cibiyar Carter da ke Amurka, ta ce babu wata shaida da ke nuna yin kutse ta yanar gizo.
Sakamakon zaben na matakin rumfuna da 'yan adawa suka wallafa, ya nuna cewa Gonzalez Urrutia mai shekaru 74, wani jami'in diflomasiyya mai ritaya, ya doke Maduro da kashi 67% na kuri'un da aka kada.
Kotun kolin Venezuela, wadda ake yiwa kallon ‘yar amshin shatar Maduro, a ranar Alhamis ta tabbatar da sake zabensa a wani wa’adin mulki na 3 mai tsawon shekaru shida, tare kuma da tuhumar Gonzalez Urrutia kan kin bayyana kamar yadda aka umarce shi.
Dandalin Mu Tattauna