An kama Pavel Durov, hamshakin attajirin da ya kafa manhajar aikewa da saƙwanni ta Telegram, a filin jirgin saman Bourget da ke wajen birnin Paris a yammacin jiya Asabar, kamar yadda gidajen talabijin na TF1 da BFM suka ruwaito, daga wasu majiyoyin da ba’a bayyana sunayensu ba.
Telegram, wanda ke da tasirin gaske musamman a kasashen Rasha, Ukraine da kuma tsohuwar Tarayyar Soviet, na daya daga cikin manyan shafukan sada zumunta bayan Facebook, YouTube, WhatsApp, Instagram, TikTok da WeChat.
Kafar ta kuma kama turbar samun masu amfani da ita biliyan 1 a shekara mai zuwa.
Durov ɗan kasar Rasha ne ya kafa Telegram tare da mazauninsa a Dubai. Ya bar Rasha ne a shekara ta 2014 bayan ya ki biyan bukatun gwamnati na rufe shafukan ‘yan adawa a dandalin sa na sada zumunta na VK, wanda ya sayar.
Durov na tafiya ne a cikin jirginsa, in ji kafar ta TF1 a shafinta na yanar gizo, inda ta kara da cewa an kai masa samame ne da sammacin kama shi a Faransa a wani bangare na binciken farko na ‘yan sanda.
TF1 da BFM duk sun ce binciken ya karkata ne kan rashin masu kula da daidaita al’amura a Telegram, kuma 'yan sanda sun dauka cewa wannan lamarin ya ba da damar aikata laifuka da ke ci gaba da gudana ba tare da daukar mataki ba a manhajar ta aika saƙwanni.
Kamfanin na Telegram bai amsa bukatar kamfanin dillancin labarai na Reuters don yin sharhi kan lamarin ba. Haka su ma ma'aikatar harkokin cikin gida ta Faransa da 'yan sanda ba su ce komai ba.
Ofishin jakadancin Rasha da ke Faransa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Rasha na TASS cewa, mutanen Durov ba su tuntubi ofishin ba bayan rahotannin kama shi, amma tana daukar matakai na gaggawa don fayyace lamarin.
Dandalin Mu Tattauna