Hukumar ta ce yanzu za a yi gasar ne a cikin watan Agustan 2025.
A baya an shirya yin gasar mai wakilcin kungiyoyi 19 ne daga ranar 1 zuwa 28 ga watan Fabrairu.
Sai dai, bayan binciken da hukumar CAF ta gudanar a kasashe uku masu daukar bakwancin wasan, ta gano ba su kammala shirin daukar nauyin gasar ba, saboda rashin filayen wasa, da wuraren horar da ‘yan wasa da kuma asibitotci.
Domin bai wa wadannan kasashen damar inganta gine-ginen su, CAF ta yanke shawarar dage gasar zuwa cikin watan Agustan 2025.
A wata sanarwa, shugaban hukumar CAF Dr. Patrice Motsepe ya tabbatar da cewa wannan gasa ta 2024, za a gudanar da ita a cikin watan Agusta da Zarar kasashen uku sun kammala inganta gine-ginensu wanda a halin yanzu suke ci gaba da aiki.
“Na gamsu da yadda ayyukan gine-ginen ke tafiya da kuma gyare-gyaren wuraren wasanni da wasu gine-gine a kasar Kenya, Tanzania da kuma Uganda,” in ji Dr. Motsepe.
A cikin kasashe uku masu daukar nauyin gasar, Kenya tana buga wasanninta na cikin gida ne a wata kasa, saboda rashin filayen wasa da CAF ta amince da su.
Gasar CHAN ta 2025 za ta zama zakaran gwajin dafi ga Kenya, Tanzania da Uganda, wadanda dukkansu suka shirya tsaf domin daukar bakuncin wasannin karshe na gasar cin kofin Afirka (AFCON) ta shekarar 2027.
A halin da ake ciki kuma, a yau Laraba 15 ga watan Junairu 2025 ne za a shirya jadawalin gasar CHAN da aka dage a birnin Nairobi na kasar Kenya