Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ademola Lookman Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan CAF Ta Bana


Lookman wanda ke taka leda a kungiyar Atalanta dake buga gasar Serie A ta kasar Italiya ya dauki hankula bayan da ya zura kwallaye 3 a wasan karshe na gasar Europa wacce kulob din nasa ya lashe.

Dan wasan Najeriya da ya yi fice a kungiyar Atalanta a gasar Serie A na Italiya Ademola Lookman, ya lashe kyautar lambar yabo ta CAF na shekarar 2024, yayin bikin karrama ‘yan wasa da hukumar kwallon kafar Afirka ta shirya wanda ya gudana a ranar Litinin, 16 ga watan Disamba a birnin Marrakech na kasar Morocco.

Lookman wanda ke taka leda a kungiyar Atalanta dake buga gasar Serie A ta kasar Italiya ya dauki hankula bayan daya zura kwallaye 3 rigis a wasan karshe na gasar Europa wacce kulob din nasa ya lashe.

Lookman ya yi takara tare da Simon Adingra (da ke bugawa kasar Ivory Coast da kungiyar Brighton da Hove Albion wasa) da Serhou Gulrassy (da ke bugawa kasar Guinea da kungiyar Borussia Dortmund wasa) da Achraf Hakimi (da ke bugawa kasar Morocco da kungiyar PSG wasa).

A fannin mata kuma Babra Banda ta Zambia ce ta lashe gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka ta 2024.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG