A ranar Alhamis da ta gabata ne aka kammala zagaye na farko na gasar cin kofin Afirka dake gudana a kasar Kamaru. Babban abin mamaki shi ne ƙasar Algeria da aka yi waje da ita wacce take rike da kofi, bayan karawar ta da ƙasar Ivory Coast. Inda aka lallasa ta ci 3 da 1.
Duk ƙasashen da suka zo na daya da na biyu a rukuninsu sun yi nasarar zuwa zagaye na gaba, yayinda ƙasashe hudu da suka zo a matsayi na uku da cin kwallo mai yawa suka yi nasarar cikata ƙasashe 16 na zagayen gaba.
Hukumar CAF ta fitar da jadawalin yadda wasannin zagaye na biyu za su kasance: Anan ne Burkina Faso za ta kara da Gabon, sai Najeriya da Tunisia, Guinea kuma za ta fafata da Gambia, yayin da za a kece raini tsakanin Kamaru mai masaukin baki da Comoros.
Sauran wasannin na zagayen, sun hada da karawa tsakanin Senegal da Cape Verde, sai Morocco da Malawi, Ivory Coast za ta fafata da kasar Masar, yayin da Mali za ta kece raini da Equatorial Guinea.
Wasannin dai za a fara su daga ranar Lahadi mai zuwa da karawar Gabon da Burkina Faso da la'asar. Sai kuma Najeriya da zata kara da Tunisia da ƙarfe 8 na yamma agogon Najeriya da Kamaru.
Saurari rahoto cikin sauti daga Mohamed Ladan: