Ana can ana ci gaba da kidayar kuri’u a Burundi, bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a jiya Talata, wanda sanadiyarsa dubban mutane suka tsere daga muhallansu cinkin ‘yan watannin da suka gabata domin gujewa aukuwar mummunan rikici.
Rahotanni sun ce ba a samu bayyanar masu kada kuri’a da dama a rumfunar zaben ba, wanda ya kasance cike da rudana ya kuma fuskanci kauracewar bangaren ‘yan adawa.
A ranar Alhamis mai zuwa ake sa ran za a fara bayyana sakamakon zabe, duk da cewa zaben ya sha sukar rashin sahihanci.
Zaben dai ya gudana duk da kiray-kirayen da kasashen duniya suka yi na cewa a dage zaben bisa dalilan mummunar zanga zanga da kasar ta fuskanta a ‘yan watannin na.
Jami’an gwamnati sun ce akalla mutane uku ne suka mutu, ciki har da wasu ‘yan sanda biyu, a wani fadan bindiga da tashin bama-bamai da suka auku gabanin zaben.