Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce harin jirage mara matuka da aka kai kan Hadaddiyar Daular Larabawa wadanda suka yi sanadin wata fashewa da tashin wutar da ta kashe mutane abin damuwa ne.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Buhari, Malam Garba Shehu ya fitar a ranar Talata, shugaban na Najeriya ya ce irin wadannan hare-hare na rutsawa da mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba da kuma gine-gine fararen hula.
“Wannan abu ne da duniya ya kamata ta yi Allah wadai da shi, ya kuma zama dole a dakatar da shi.” Buhari ya ce.
A ranar Litinin mayakan Houthi suka kai hari kan wajen birnin Abu Dhabi a matsayin martani kan rawar da kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa take takawa a yakin Yemen.
“A madadin gwamnati da al’umar Najeriya, muna mika sakon jajenmu ga al’umar kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa.” Shugaban Buhari ya kara da cewa.
Bayan harin na ranar Litinin, mayakan na Houthi, sun kuma yi gargadin cewa za su kuma kaikaitar wasu wurare a kasar ta Hadaddiyar Daular Larabawa.
Sai dai Shugaban na Najeriya ya yi kira da a kai zuciya nesa ta hanyar rungumar matakan hawa teburin tattaunawa.